Halin Matsin Rayuwa Lokacin Ramadan
Wani Shehin Malami ya fashe da kuka sakamakon wata tambaya da akayi masa lokacin karatu a watan Ramadan. Tambayar tana cewa: "Allah ya gafarta Mallam, shin azumin mutum zai karbu ba tare da buɗa baki ko kuma sahur ba?".
Just imagine; wato tsananin rashi da kuma matsi na rayuwa ya sanya mutum zai dauki azumi ya yini har zuwa lokacin buda baki ba tare da yana da wani abu da zaiyi buda baki dashi ba. Haka nan washegari, zai kuma daukar wani azumin ba tare da yayi Sahur ba domin bashi da abinda zaici. Innalillahi waina ilaihirrajiun!!!
Yau muna kwana na shida a wannan wata me alfarma wato watan Ramadan. Kuma na tabbata ba za a rasa irin wannan mabuƙatan a inda muke rayuwa ba; wala a kusa damu, ko kuma a nesa damu.
Dan Allah jama'a ayi ƙokari wajen ganin an taimakawa al'umma a wannan lokaci na tsanani da kuma matsi. Ba wai se kana dashi da yawa ba. Ko yaya yake ka bayar, domin wani wannan ya rasa.
Allah ya bamu ikon taimakawa.
Salisu Musa Rabiu.
Comments
Post a Comment